Hukumar Shirya Jarrabawar kammala Sakandare ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta shekarar 2021 (SSCE).
Shugaban hukumar ta WAEC a Najeriya Patrick Areghan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
Areghan ya bayyana cewa mutane 1,573,849 ne suka yi rijistar WASSCE a fadin makarantun sakandire 19,425 da aka amince da su a kasar nan, yayin da 1,560,261 suka zana jarrabawar.
A cewarsa, 1,274,784 daga cikin daliban sun samu kiredit biyar ko sama da haka a darusa daban daban,, da suka hada da Ingilishi da Lissafi, yayin da dalibai 1,560,261 suka samu kiredit da sama da haka a cikin mafi karancin darussa biyar — wato tare da ko babu Ingilishi da lissafi.
Ya kuma ce an ruke sakamakon Dalibai 170,146 da ake zargi da hannu a badakalar jarabawar.
Ya kara da cewa hukumar WAEC ta riga ta tantance tare da fitar da sakamakon mutane 1,256,990 wanda ke wakiltar kashi 80.56% na wadanda suka zana jarrabawar a Najeriya.
Areghan ya kuma ce har yanzu WAEC na ci gaba da tantance sakamakon dalibai 303,271 wanda ke wakiltar kashi 19.44 na adadin wadanda suka yi jarabawar a kasar nan.
“Jarabawa, wadda ta kasance ta kasa da kasa, an yi ta ne a lokaci guda a cikin kasashe biyar na Nahiyar, – Gambia, Ghana, Laberiya, Najeriya da Saliyo, ta hanyar amfani da jadawalin kasa da kasa guda daya.”