Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da cewa za ta gudanar da wani karin zabe a mazabar Doguwa/Tudun Wada ndake jihar Kano.
Wannan shawarar ta zo ne bayan da jami’in tattara sakamakon zaben mazabar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, Ibrahim Yakasai ya sake duba kan sakamakon zaben da aka gudanar a yankin.
KU KARANTA: Da Dumi-Dumi: Mummunan Zanga-Zanga Ta Barke A Jojiya
A cewar Yakasai, hukumar ta sake duba sakamakon farko da ake zargin sa ya bayyana ta hanyar tursawa Ya bayyana cewa INEC ta bi ka’idojin dokar zabe kuma ta sake duba sakamakon zaben.
Da yake bayyana sakamakon da aka sake dubawa, ya bayyana cewa “sakamakon zaben da aka duba ya nuna cewa, APC na da kuri’u 39,732, NNPP na da 34, 798, yayin da PDP kuma ke da 7,091.” Ya kuma bayyana cewa an soke sakamakon zabe a rumfunan zabe 13 dake mazabar.
Ya kara da cewa “jimillar kuri’un da aka soke a rumfunan zabe da aka soke sun fi tazarar dake tsakanin jam’iyyar APC da NNPP”
Ya kuma bayyana cewa adadin katunan zabe na dindindin (PVCs) da aka karba a rumfunan zabe 13 da aka soke sun kai 6,917 sabanin kuri’u sama da 4,000 da ke tsakanin APC da NNPP.
Yakasai ya ce INEC za ta gudanar da karin zabe a sassan da abin ya shafa domin tantance wanda ya lashe zaben mazabar tarayya na Doguwa/Tudun Wada da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairu.
Idan ba a manta ba dai, Hukumar zabe ta kasa INEC ta cire sunan shugaban majalisar wakilai Alhassan Ado Doguwa wanda ya fito daga mazabar daga jerin sunayen wadanda suka lashe zaben.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito yadda aka kama Doguwa bisa zarginsa da hannu wajen kashe wasu mutane da kuma kona sakatariyar jam’iyyar NNPP dake yankin.
Daga bisani an tasa keyar dan majalisar zuwa gidan yari na Kano amma aka bayar da belinsa.
A wani labarin kuma, Buhari ya taya Farfesa Osinbajo murnar cika shekaru 66 a duniya
A yau Laraba Shugaba Muhammadu Buhari ya taya mataimakin sa Yemi Osibanjo muranar zagayowar ranar haihuwar karo na 66. Kamar yadda Guardian ta ruwaito.
Shugaban kasar ya yaba wa Osibanjo kan yadda ya haɗa wasu ayyukah da gudanar da sha’anin mulki.