Wani tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani, ya janye daga takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Nnamani ya bayyana janyewar sa ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai a Abuja ranar Litinin.
Tsohon dan majalisar ya ce: “A halin da ake ciki yanzu babu wata ma’ana a gare ni in ci gaba da takara domin ban samu damar tallata bayanana da ra’ayoyina ga wakilan jam’iyyarmu ta hanyar da za a iya yin shawarwari ba.
“Saboda haka, na dakatar da burina, ina yi wa jam’iyyar fatan samun nasarar gudanar da zaben fidda gwani da hadin kai domin mu samu nasara a babban zaben 2023.
“Zan ci gaba da yin cudanya da jam’iyyar da shugabanninta domin ganin cewa tunani da dabi’un da nake ji da su da yadawa sun samu gindin zama a cikin harkokin mulkin jam’iyya da shugabancin jama’a bayan zabe.”
A halin yanzu, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan a matsayin dan takarar jam’iyyar.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ta fara zaben fidda gwani na shugaban kasa a Abuja babban birnin kasar