Biyo bayan wani mummunan harin da aka kai ranar Lahadi a cocin Saint Francis Catholic Church, Owo a jihar Ondo, babban Fasto na Awaiting The Second Coming Of Christ Ministry, Adewale Giwa, ya bayyana cewa lamarin da aka samu manuniya ce ta durkushewa kasar nan a karkashin jam’iyyar APC.
A cewar Fasto wanda ya nuna alhininsa kan kisan da ‘yan bindiga suka yi wa masu ibada, shugaban kasa Muhammadu Buhari bai kawo komai ba sai bakin ciki ga Najeriya.
Giwa ya yi magana ne a lokacin da yake mayar da martani kan harin da aka kashe mutane da dama.
Ya kara da cewa, ya na ta bayani kan tada hankali da ayyukan da makiyaya ke yi a jihar, inda ya ce babu inda za a samu tsaro a kasar.
“Mummunan lamari a tarihin jihar Ondo. Idan za a iya tunawa, a ranar 8 ga Janairu, 2022, na shawarci Gwamna Oluwarotimi Akeredolu kan matsalar tsaro.
“Musamman na kuma tayar batu kan ayyukan makiyaya a jihar. Wannan abin takaici ne.
“Najeriya ta durkushe a karkashin gwamnatin APC. A baya na bayyanawa ‘yan Nijeriya cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa ‘yan uwansa fulani ikon ta’addancin da kashe ‘yan kasa da ba su ji ba gani ba.
“Ta yaya wani zai tashi ya je ya bauta wa Allah, amma ya kasa komawa gida lafiya?
“A Najeriya a yau, da kyar ka yi barci da idanunka biyu a rufe saboda gazawar gwamnati mai ci wajen samar da mafita mai ɗorewa ga matsalolin tsaro na ƙasar.
“A tsawon shekaru, wannan gwamnatin ta kawo wa kasa ciwo, radadi da bala’i. Addu’ata tana tare da iyalan wadanda abin ya shafa.”