Dan takarar sanata na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi alkawarin cewa majalisar dattawa ta 10 za ta hada kai da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wajen biyan basussukan da ake bin kasar, The Nation ta rawaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Guda Cikin Ayarin Motocin Wani Gwamna Ta Banke Babur, 3 Sun Kwanta Dama
Akpabio ya yi wannan alkawarin ne a wata ganawa da ya yi da kungiyar Sanatocin APC masu zaman kansu a Abuja.
Akpabio ya godewa tsaffin ‘yan majalisar bisa amincewar da suka yi masa, ya kuma yi alkawarin tabbatar da amincewar da suka yi masa bayan an zabe shi a matsayin shugaban majalisar dattawa.
A wani labarin kuma, Nimi Briggs Ya Yi Aiki Tukuru Domin Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU na 2022 – Buhari
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Talata ya yaba da kokarin marigayi malami Emeritus Farfesa Nimi Briggs, game da kudurorin da suka kai ga warware yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta fara a shekarar 2022,Punch ta rawaito.
Buhari ya bayyana marigayi Emeritus Farfesa a matsayin malami mai kishin kalandar ilimi a jami’o’in Najeriya.
Buhari wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar sa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya bayyana hakan a wurin taron tunawa da Briggs, a Abuja.
“A cikin manyan bangarorinsa guda biyu na gwaninta – ilimi da likitanci daya yi fice. Ya kawo iya rayuwarsa marar misaltuwa zuwa fage na matsayi na ilimi.
“Ya kamata a ambaci godiyarsa bisa jagorancin tawagar gwamnatin tarayya na tattaunawa da kungiyoyin kwadagon mu kan inganta tsarin jami’o’inmu a kasar nan a shekarar 2022.