An tabbatar da mutuwar wasu mutane uku ‘yan asalin karamar hukumar Ezza ta Kudu bayan da ayarin motocin gwamnan jihar Ebonyi David Umahi suka afkawa wani babur a kan hanyar filin jirgin saman kasa da kasa na Muhammadu Buhari,Punch ta rawaito.
Rahotanni sun bayyana cewa sun ajiye gwamnan jihar a filin jirgin da ke Onueke, kuma a lokacin da suke komawa garin, lamarin ya faru.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwana Ya Kare: Yan Jarida Biyu A Najeriya Sun Kwanta Dama
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne jim kadan bayan bude gadar sama mai suna Prince Arthur Eze a Abaomege da ke karamar hukumar Onicha.
Prince Arthur Eze tare da Gwamna Umahi ne suka kaddamar da gadar saman.
Daga nan ne aka samu labarin cewa jim kadan bayan kammala taron gwamnan ya tafi Abuja.
Sai dai kuma Prince Arthur Eze da mataimakin gwamnan jihar Eric Kelechi Igwe sun bar wurin da hatsarin ya afku inda suka jajanta wa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su kafin su ba da umarnin a kai su asibiti sannan su wuce jihar Enugu.
Babur din wanda abin ya rutsa da su da motar Sienna da abin ya shafa sun lalace ba za a iya gyara su ba, duk da cewa ba a san sunayensu da lambar rajistar motar da aka yi rashin sa’a ba har zuwa lokacin da aka gabatar da wannan rahoton.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Dira a Abuja Daga Kasar Waje
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya isa Abuja daga birnin Landan na kasar Birtaniya, inda ya yi jinyar hakora a makon da ya gabata.
Jirgin Gulfstream ne ya kai Buhari bangaren shugaban kasa na filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.