Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta tsige mataimakin Gwamnan Jihar Barista Mahdi Aliyu Gusau.
Majalisar ta dauki wannan matakin ne, bayan da aka Mika rahoto na musamman da aka Tara dangane da binciken da ake Kan mataimakin Gwamnan.
Mambobi 20 cikin 24 Kuma sun amince da tsige shi, Wanda hakan ya bayar da damar tube shi daga mukamin.
Kakakin Majalisar Nasiru Muazu Magarya ne ya sanar da hakan yau, yayin zaman Majalisar.
A baya dai, mataimakin Gwamnan yayin hirarsa da BBC ya ce zasu tsige shi domin yaki sauya Jam’iyya Kamar yadda Gwamnan Jihar yayi.