Majalisar Malamai ta Jahar Kano ta sanar da dakatar da sanannen Malamin nan Sheikh Ibrahim Khalil wanda kuma shine shugaban ta.
Majalisar ta kuma musanya shi da Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan a matsayin shugaban Majalisar, wanda Majalisar ta zarge shine, a dalilin zargin shi da siyasantar da harkokin Majalisar, tare da amfani da matsayin sa domin amfanin kanshi.
Malamai da Ƙungiyoyin Addini da suka ƙunshi Tijjaniya, da Ƙadiriyya da Izala suka sanar da matsayar su a taron Manema labaru daya wakana a Sakatariyar Ƙungiyar Ƴan jarida ta Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Neja: Rundunar ‘Yan Sanda Sun Cafke Wadanda Ake Zargi Da Sayar Da Man Fetur Ga ‘Yan Bindiga
Dayake jawabi ga Manema labaru, Shugaban Ƙungiyar Haɗakar Malaman Addini, Imam Jamilu Abubakar yace sun yanke shawarar tsige Sheikh Ibrahim Khalil daga Shuwagabancin Ƙungiyar sabudda shiga harkokin siyasa.
Imam Abubakar yayi nuni dacewar, sanannen Malamin ya kasance yana shiga siyasa tun a zamanin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, da Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma ta. Ganduje.
Sunce yaso ya tsaya takarar Gwamna a Gwamnatocin da suka gabata, kuma yace idan bai samu tikitin tsayawa takara a Jami’iyya maici sai ya fita daga harkokin gwamnatin dake ci a lokacin.
Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan wanda kuma shine shugaban Hukumar kyautata jindadin Alhazai ta Jaha kuma Babban Limamin Masallacin Sheikh Jaafar Mahmud dake Tudun Murtala, kuma ya kasance abokin tafiya ne a Gwamnatin Jahar Kano Maici a yanzu, ƙarƙashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje kafin naɗin shi.