Rahotanni sun bayyana cewa ministan babban birnin tarayya na farko Cif Mobolaji Ajose-Adeogun ya rasu, Punch ta rahoto.
Dan kasuwar mai shekaru 96 ya mutu a ranar Asabar 1 ga watan Yuli 2023.
KARANTA WANNAN: Wasu Matasa 2 Sun Samu Gurbi A Gidan Yari Bisa Laifin Kutse a Gidajen Mutane
Daya daga cikin dangin gidan mai suna Oluremi Ajose-Adeogun ne ya tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da ya rubuta a madadin iyalan wanda wakilinmu ya samu a ranar Litinin.
An karanta, “Iyalan Cif Mobolaji Ajose-Adeogun sun sanar da rasuwa zuwa madawwamiyar daukakar uban gidansu, kakansu, Cif Mobolaji Ajose-Adeogun, FCIS, CON, JP.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tuna cewa Gwamnatin mulkin soja ta Janar Murtala Mohammed ta nada shi minista kuma shi ne ke da alhakin gudanar da babban tsarin Abuja a lokacin yana ministan babban birnin tarayya Abuja.
“Kafin a nada shi ministan babban birnin tarayya, Cif Mobolaji Ajose-Adeogun ya yi aiki mai inganci a matsayin kwamishinan hadin gwiwa da samar da kayayyaki na tarayya na wa’adi biyu a watan Agustan shekarar 1975.
Sanarwar ta kara da cewa “Daga baya an nada shi kwamishinan ayyuka na musamman na gwamnatin tarayya, hukumar raya babban birnin tarayya.”
Har zuwa rasuwarsa, Ajose-Adeogun ya kasance shugaban Ita-Aladan, Obun Eko, Isale Eko, Legas kuma ya yi fice a kamfanin Shell Petroleum Development da kuma masana’antu da gidaje.
A wani labarin kuma, Tinubu Ya Gana Da Tawagar Wani Kamfanin Masu Zuba Jari A Aso Villa
Taron na ranar litinin ya biyo bayan komawar Tinubu Abuja ranar Lahadi bayan da ya gudanar da bukukuwan babbar Sallah a Legas a makon jiya.
Shugaban kasa, Bola Tinubu, a ranar Litinin din nan ya karbi bakuncin tawaga daga kamfanin raya man fetur na Shell a babban dakin taro na Aso Rock da ke Villa a Abuja.