Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi-Magashi (mai ritaya) ya bada tabbacin cewa nan bada jimawa za su kwato daliban da aka sace a wata makarantar Sakandare ta gwamnati a garin Kankara dake jihar Katsina.
Ministan ya bada wannan tabbacin ne a ranar Lahadi a Katsina a yayin da ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa ga gwamnan jihar, Aminu Masari domin jajanta masa bisa abin da ya faru.
Ya bada tabbacin cewa jami’an tsaro suna aiki tukuru wajen ganin sun kwato wadannan dalibai da aka yi garkuwa da su.