By Abbas Yakubu Yaura
Tsohon mashawarcin fasaha na hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF), Augustine Eguavoen, an sauke shi daga mukaminsa ba tare da bata lokaci ba.
Hakan ya biyo bayan gazawar da kungiyar Super Eagles ta Najeriya ta yi na samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2022, bayan da suka tashi 1-1 da Black Stars ta Ghana a filin wasa na Moshood Abiola na kasa da ke Abuja ranar Talata.
DUBA WANNAN LABARIN: Hatsarin Jirgin Ruwa: An Samu Gawarwakin Mutane 13 Yayin Da Hukumar SEMA Ke Cigaba Da Aikin Ceto
‘Yan wasan kasar Ghana sun dauki tikitin ne a kan dokar jefa kwallo a waje bayan sun yi kunnen doki da kungiyar ‘yan wasa ta Super Eagles a ranar Asabar a karawar farko a filin wasa na Baba Yara, dake Kumasi.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Daraktan yada labarai na NFF, Ademola Olajire, ya ce a halin yanzu NFF ta janye kwantiragin shekaru biyu da rabi da aka yi wa kociyoyin tare da soke nadin daukacin ma’aikatan hukumar nan take.
“Za a sanar da sabbin ma’aikatan hukumar bayan an yi nazari na tsanaki don jagorantar sabon aikin karfafa kungiyar Super Eagles don fuskantar kalubale nan gaba yadda ya kamata.”
Babban sakataren NFF Dakta Mohammed Sunusi, a cikin sanarwar daya fitar yace “Muna godiya ga masu horar da ‘yan wasa da jami’an kungiyar bisa hidimar da suke yi wa kasa kuma muna yi musu fatan samun nasara a harkokinsu na gaba,”
Kazalika ana sa ran Eguavoen mai shekara 56 da ya horar da tawagar har sau biyu zai koma tsohon muƙaminsa na daraktan wasanni.