Wani bangare na jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin Manjo Agbo, ya kori dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Sanata Rabi’u Kwankwaso, bisa zarginsa da ayyukan cin amana da kuma karkatar da kudaden yakin neman zaben jam’iyyar.
Sakataren yada labaran jam’iyyar NNPP, Abdulsalam Abdulrasaq ne ya sanar da korar Kwankwaso a wata sanarwa da ta fitar a Abuja ranar Talatar nan.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Wannan lamarin na zuwa ne kwanaki uku bayan da shugabannin bangarorin suka sha alwashin bincikar tsohon gwamnan Kano da wasu masu yi masa biyayya a kan zargin almubazzaranci da sama da Naira biliyan daya da aka samu daga sayar da fom din takara.
Amma Abdulrasaq ya tabbatar da cewa an dauki matakin korar Kwankwaso ba tare da bata lokaci ba bayan ya kasa gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa don kare kansa kan zargin ‘munanan ayyukan da ya yi wa jam’iyya da kuma karkatar da kudaden yakin neman zaben jam’iyyar cikin kwanaki biyar.
Sai dai kakakin ya sake nanata cewa korar tasa ta yi daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyar na 2022 da aka yi wa kwaskwarima.
KARANTA WANNAN Dubban MagoyaBayan NNPP Sun Tarbi Kwankwaso A Kano
Ya ce, “Kwamitin zartaswa na kasa ta yi zaman gaggawa a ranar Juma’a, 1 ga watan Satumba, inda ta yanke shawarar cewa, bayan kin bayyanar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a gaban kwamitin ladabtarwa da ya zauna a ranar Alhamis 31 ga watan Agusta, bayan an gayyace shi a rubuce, don haka an kore shi daga NNPP nan take.
“Za a kai rahoton tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zuwa wuraren da suka dace domin amsa tambayoyi kan rashin bayanin kudi da suka shafi almubazzaranci da dukiyar al’umma.”
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Da yake mayar da martani, wani abokin Kwankwaso kuma mai binciken kudi na kasa na NNPP, Ladipo Johnson, ya fusata da rahotan inda ya ce bangaren Agbo ba su da hurumin korar tsohon gwamnan.
“Korar waye? Waɗannan mutanen ba mutanenmu ba ne. Sun fita daga jam’iyyar kuma ba za su iya magana a madadin jam’iyyar ba. Su kafa jam’iyyarsu ko kuma su je kotu. Yana da sauƙi kamar wancan. Akwai muhimman abubuwa da yawa da ya kamata a damu da su a wannan ƙasa.
“Ta yaya za su kori Kwankwaso? Shin akwai wanda dangantakarsa da kwamitin ayyuka ta kasa ta kasance a nan shedkwatar kasa da ke Abuja? Nan ba da dadewa ba za mu yi taron manema labarai don shawo kan lamarin,” inji shi.
A Wani Labarin Kuma Ofisoshin Gwamnati A Abuja, Da Wasu Sun Rufe Yayin Da NLC Ta Fara Yajin Aiki
A halin yanzu an rufe wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati a Abuja domin nuna goyon bayansu ga yajin aikin kwanaki biyu da kungiyar kwadago ta Kasa NLC ta ayyana a fadin kasar, inji rahoton jaridar The PUNCH.
Wakilinmu da ya ziyarci sakatariyar gwamnatin tarayya a safiyar ranar Talatar nan tare da wasu manyan wurare kamar gidan rediyo mai farin jini da ke da wasu hukumomi a karkashin ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a ta kasa.