Yanzu-Yanzu: Osinbajo na ganawa da Shugaban APC, da Gwamnoni 5
Mataimakin Shugaban Ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo a halin yanzu yana taron da aƙalla Gwamnoni 5 na Jam’iyyar APC da Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba don ni ba, da Buhari bai zama Shugaban Ƙasa ba a 2015 – Cewar Tinubu
Taron ya zo ne kwanaki bayan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yayi taro da Gwamnoni a ɗakin taro na Villa a ranar Talata, kafin ya bar Ƙasar zuwa Ƙasar Spaniya.
Taron ya kuma zo ne bayan kammala tantance dukkanin ƴan Takarar Shugaban Ƙasa da Kwamitin John Odigie-Oyegun ya Jagoranta.
Duk da ba’a bayyana wane Gwamnoni ne yake taron dasu ba, Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa taron yana wakana a ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa.