Gwamnan Jahar Lagos Babajide Sanwa-Olu ya Hana dukkanin nau’in Acaɓa da akafi sani da Okada a Ƙananan Hukumomi 6.
Gwamnan ya sanar da cewa an hana Acaɓa ne gaba ɗaya.
Ƙananan Hukumomin kamar yadda Gwamnan ya bayyana sun haɗa da Ikeja, da Surulere, da Eti-Osa, da Lagos Mainland, da Lagos Island, da kuma Apapa.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Kashe Mutum 5, An Bankawa Gidaje Wuta, Yayin Rikicin Yan Kasuwa Da Yan Okada A Abuja
Gwamnan ya bada umarnin ne a taron da yayi da Kwamishinan Ƴan Sanda, dana Area Kwamanda, da DPO a gidan Gwamnatin dake Alausa.
Sabuwar Dokar hana Acaɓa ya biyo bayan hana aikace-aikacen Acaɓa a watan Fabrairu na Shekarar 2020.
Sanwa-Olu yace Gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne da yayi dai-dai da Dokar Sufuri ta Shekarar 2018 domin magance faɗa ce-faɗa ce da aka ƙirƙira akan Okada.
Ya shaidawa ƴan sanda dasu tabbatar da Dokar ba tare da wani ɓata lokaci ba.
Yace “bayan yin dubi akan hana Acaɓa a Ƙananan Hukumomi guda 6 da muka santa a 1 ga watan Fabrairu na Shekarar 2020, munga har yanzu ba’a daina ba. To yanzu mun hana yin Acaɓa a dukkanin manyan hanyoyi da gadoji a cikin waɗannan Ƙananan Hukumomin guda 6, wanda Dokar zata fara daga 1 ga watan yunin Shekarar 2022.
Hana Acaɓa ya biyo bayan kashe wani Matashi da ƴan Acaɓa suka yi a yankin Lekki ta Jahar Lagos akan Naira 100.
Ɗan Acaɓan dai ya kasance Injiniya ne wanda aka kashe tare da ƙonawa akan Naira 100 da wani Ɗan Acaɓa.
Comments 1