By Abbas Yakubu yaura
Allah yayiwa Sarkin Ban Kano kuma tsohon kwamishinan ilimi na farko a Kano, Alhaji Mukhtar Adnan ya rasu.
Hakimin Dambatta, Mukhtar Adnan ya rasu ne da sanyin safiyar Juma’a bayan gajeriyar rashin lafiya kamar yadda majiyar ‘yan uwan sa ta bayyana.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa tsohon Sarkin Kano, Sir Muhammadu Sanusi shine wanda ya nada Mukhtar Adnan a matsayin Sarkin Bai a shekarar 1954 domin ya gaji mahaifinsa.
A cewar wani masanin tarihi kuma marubuci kan masarautan Kano, Ibrahim Ado Kurawa, yace an haifi Adnan a shekarar 1926.
Sannan ya yi makarantar Elementary ta Dambatta da makarantar Middle Kano da kuma makarantar malamai ta Zariya.
Sannan kuma ya fara aiki ne a karamar hukumar Kano inda ya yi ayyuka daban-daban kafin hawansa mukamin Sarkin Bai.kuma ya kasance dan majalisar wakilai ta tarayya a jamhuriya ta farko.
Sannan kuma an nada shi Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano na farko a shekarar 1968.
Adnan ya kasance memba mafi dadewa a Majalisar Masarautar Kano tun kafuwar Masarautar a karni na 19 kuma kamar kakansa Dabon Dambazau, wanda ya kasance memba mafi dadewa a cikin karni na 19.
Kazalika ya yi shekara sittin da uku a matsayin hakimi, Kansila da kuma dan majalissar Sarki.
Ya halarci zaben sarakuna uku, Sarkin Kano Muhammadu Inuwa a shekarar (1963), Sarkin Kano Ado Bayero da shekarar 1963-2014, sai Sarkin Kano Muhammad Sanusi a shekarar (2014-) da kuma Sarkin Kano Aminu Bayero a 2020.