By Abbas Yakubu yaura
Shugaban hukumar kashe gobara ta tarayya Dakta Liman Ibrahim Alhaji yace Najeriya bata da manufar kashe gobara bayan shafe shekaru 100 tana aikin hukumar kashe gobara a kasar.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, a gidan gwamnati dake Minna.
Yace ya je jihar ne domin komawa baya da nufin samar da takardu kan manufofin kashe gobara, na (SOP) da kuma ladabtarwa na hukumar kashe gobara ta tarayya.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Gwamnan ya yi kira da a kafa hukumar kashe gobara ta tarayya a muhimman wurare na gwamnatin tarayya a fadin kasar nan dan magance matsalolin tashin gobara.
Kazalika ya yi nuni da cewa kasancewar hukumar kashe gobara ta tarayya a wurare masu muhimmanci musamman ma’ajiyar man fetur zai taimaka matuka idan aka samu matsala.