Masarautar Saudiyya ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama daga Najeriya zuwa kasar, saboda sabon cutar Coronavirus, Samfarin Omicron.
A ranar Larabar da ta gabata ne wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba na cewa ana shirye-shiryen mayar da ‘yan Najeriya mazauna Masarautar kasar su, kan Omicron.
Sai dai wasu majiyoyi da dama a karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Kano da kuma jami’ai a filin jirgin saman Malam Aminu Kano (MAKIA) sun tabbatar wa majiyar Jaridar Simokuradiyya cewa an bayar da umarnin takaita zirga-zirgar jiragen sama daga Najeriya zuwa Saudiyya Saboda cutar Corona Nau’in Omicron.
Tun bayan da Masarautar ta dage dokar hana zirga-zirgar jiragen sama na Najeriya, mutane da dama musamman daga Kano sun je kasar don gudanar da aikin Umarah,, yayin da wasu ke dakon ranakun da za su ziyarci kasar Mai tsarki.
Sai dai wani jami’in ofishin jakadancin Saudiyya da ke Kano, wanda ya zabi a sakaya sunansa saboda ba a umurce shi da ya yi magana da manema labarai ba, ya shaida wa jaridar Daily Trust a ranar Laraba cewa, an bayar da umarnin takaita zirga-zirgar jiragen sama na Najeriya zuwa Saudiyya, domin duba yaduwar cutar corona Samfarin Omicron a Masarautar.
A gefe guda kuwa Wani Babban jami’i a filin tashi da saukar jiragen sama na Kano ya kuma tabbatar wa da wakilin Majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa, tuni aka fitar da wata sanarwa cewa, an soke duk wasu kananan tafiye-tafiyen aikin Umarah saboda wannan yanayi da ake ciki.
“Eh gaskiya ne domin an fitar da wata takarda cewa, a soke duk wasu kananan jirage dake Kai Fasinjoji Zuwa aikin Umarah, kuma ba za a kara tashi daga Najeriya ba har sai an fitar da wata sanar.”
“Ina tsammanin suna bin matakin da wasu kasashe kamar Burtaniya suka yanke na hana kamuwa da kwayar cutar a cikin masarautar,” kamar yadda majiyar mu ta ruwaito.
Sai dai daya daga cikin jiga-jigan Ma’aikatan Jirgin ya ce ba zai iya tabbatar da faruwar lamarin ba, yayin da jiragen biyu na kasar Qatar wato Badar Air suka bar Abuja zuwa Jeddah da safiyar yau Laraba.
Daga baya hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Saudiyya GACA ta tabbatar da dakatar da zirga-zirgar jiragen a cikin wata sanarwa da ta fitar ga dukkan kamfanonin jiragen sama da ke aiki a kasar.
Daily Trust ta ruwaito cewa a halin yanzu Najeriya na da mutane shida da aka tabbatar sun kamu da cutar Corona Samfarin Omicron.
Sai dai idan za’a iya tunawa tuni Gwamnatin tarayya ta yi watsi da haramcin da Birtaniya da Canada suka kakaba wa Najeriya kan Nau’in cutar Samfarin Omicron.
Comments 1