Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuni da cewa fitaccen Malamin addinin Musulunci na Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi na ganawar sirri da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a garin Abeoukuta babban birnin jihar Ogun.
Kehinde Akinyemi, mai taimakawa Obasanjo kan harkokin watsa labarai shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Lahadi. Inda ya ce Sheikh Ahmad Gumi ya zo ne da sauran tawagar Malaman addini na kasar.
A cewar Akinyemi, Shehin Malamin ya isa gidan Obasanjo ne da misalin karfe 11 na safe. Inda ya ce daga isar sa gidan suka fara zaman sirrin.
Sai dai ba a bayyana hakikanin dalilan zaman ba, amma wadansu majiyoyi sun bayyana cewa zaman na da alaka da yunkurin Shehin Malamin na kawo karshen matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a kasar.