By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi daga Abuja zuwa birnin Londan na kasar Burtaniya domin duba lafiyarsa, wanda ake sa ran zai dauki tsawon kimanin makonni biyu.
Shugaban wanda da farko ya shirya fara tafiya zuwa birnin Landan daga birnin Nairobi na kasar Kenya, inda ya halarci bikin cika shekaru 50 na hukumar kula da muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya (UNEP), ya dawo gida a ranar Juma’ar da ta gabata.
Jirgin shugaban kasar Najeriya Air Force 1, ya tashi daga bangaren shugaban kasa na filin jirgin Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Shugaban ma’aikatan fadar sa Farfesa Ibrahim Gambari ne ya tarbo Buhari a filin jirgin sama na Karamar Ministar Babban Birnin Tarayya (FCT), Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu; da kuma Darakta-Janar na hukumar tsaro ta DSS, Yusuf Magaji Bichi.
Sauran sun hada da mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda (DIG) Sanusi Lemu, da sauran manyan jami’an gwamnati.
Mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Mista Femi Adesina, a makon da ya gabata ya yi nuni da cewa jinya ta yau da kullum a birnin Londan bata wuce makonni biyu ba.