Wani tsohon dan majalisar dokokin jihar Oyo, Tirimisiyu Okunola ya rasu.
Kanensa mai suna Bashir Okunola ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a shafin sa na Facebook.
KARANTA WANNAN LABARIN: Masu Ruwa Da Tsakin Inyamurai A Legas Sun Amince Da Dan Takarar PDP
Okunola, wanda ya wakilci mazabar Ido ta jihar a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011, a karkashin jam’iyyar ANPP, kuma daga baya ya koma jam’iyyar PDP, an ce ya rasu ne sakamakon ciwon suga.
Kanin marigayin ya rubuta a shafinsa na Facebook, “Haaaaa egbon me yasa yanzu ka bar mu da wuri.(sic) Hon.Tirimisiyu Olasupo Okunola.”
A wani labarin kuma, Allah ne kawai bai ƙaddari Shugabancin Peter Obi ba a 2023 – Ohanaeze
Babbar kungiyar al’adun kabilar Igbo, kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta duniya, ta ce shugabancin Peter Obi bai kaddara ba a 2023.
Kungiyar ta yaba da nasarar da Bola Ahmed Tinubu ya samu a matsayin zababben shugaban kasa daga zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 a Najeriya a matsayin abin faranta rai.