Dan takarar gwamna na jam’iyyar Social Democratic Party a jihar Delta, Cif Kenneth Gbagi, ya yi alkawarin gyara masakun Asaba idan aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar a zaben da za a yi ranar Asabar, Punch ta rawaito.
Gbagi ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da yake jawabi a wani gangamin da ya samu halartar fastoci daga coci-coci daban-daban da kungiyoyin mata a cikin babban birnin Asaba ranar Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Tsohon Dan Majalisar Oyo Ya Rasu
Ya bayyana cewa “A cikin shekara daya da muka yi a gwamnati, za mu gyara masakar Asaba mu maido da ita aiki. Za mu samar da kowane irin kayan tufafi. Za mu fitar da kayayyakin tufafin zuwa wasu kasashen waje.”
Gbagi ya bayyana cewa zai maido da kamfanin masaku da samar da aikin yi da kuma ci gaba da gudanar da shi, ci gaban da a cewarsa zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin Asaba da habaka kudaden shiga da gwamnatin jihar ke samu a cikin gida.
Da yake karin haske, dan takarar gwamnan na SDP ya ce gwamnatinsa za ta mayar da wani bangare na filayen Isoko zuwa wurin noman shinkafa yayin da dukkan makarantun jihar Delta za su rika gudanar da ayyukan karatu kyauta tun daga matakin firamare zuwa jami’a.
Ya koka da halin da makarantun gwamnati ke ciki a jihar.wanda ya bayyana a matsayin abin tausayi.
“Za mu gyara tsarin makarantunmu. Bayan haka, ba zan bar yaran jami’an gwamnatinmu su je makaranta zuwa kasashen waje ba. Za mu bunkasa asibitocinmu ta yadda babu wanda zai tashi zuwa kasar waje neman lafiya a wajen jihar nan,” inji shi.
Gbagi ya kuma ce a ranar 1 ga watan Yuni, 2023, zai rika biyan kowane matashin Delta Naira 30,000 duk wata. Ya yi alkawarin sarrafa kowane matashi a jihar tare da samun bayanan dukkan su.
Kazalika, ya gargadi matasan cewa kada su bari kowa ya yaudare ku da alkawuransa na banza. Gbagi yana da mafita ga kalubalen da ke faruwa a jihar Delta.”
Ya kuma yi alkawarin yi wa kowa da kowa daidai to a jihar.
“Idan na karbi mulki kuma na yi abin da suka yi, Allah zai kunyata ni. Wannan zabe ba nawa ba ne Kenneth Gbagi. Ya shafi jin dadin al’ummar jihar Delta. Dole ne mu kwato jihar Delta, mu mai da ita kishin wasu.”
A wani labarin kuma, Masu ruwa da Tsakin Inyamurai A Legas Sun Amince Da Dan Takarar PDP
A ranar Asabar din da ta gabata ne masu ruwa da tsakin kabilar Igbo a jihar Legas suka amince da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Dr Abdul-Azeez Adediran da abokin takararsa, Madam Funke Akindele a hukumance.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa shugabannin Ndigbo sun bayyana goyon bayansu ga Adediran a wani taron da aka yi wa lakabi da “Communities Igbo in Lagos Official Endorsement of Dr Abdul-Azeez Adediran”.