Shahararriyar cocin Delta, MercyLand dake kan titin Effurun-Sapele a karamar hukumar Uvwie a jihar Delta, na ci da wuta. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Har yanzu babu cikakken bayani kan abin da ya haddasa gobarar har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mu Taru Mu Dauki Kaddara — Gwamnan Taraba Ya Shawarci APC
An ga masu wucewa da gudu cikin harabar cocin Mercy City suna kuka yayin da hayaki ya turnuke sararin samani.
Har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, jami’an kashe gobara ba su je wurin kashe wutar da ta tashi ba.
Kazlaika Har yanzu ba a ga Babban Faston cocin, Jeremiah Omoto Fufeyin ba.
Akwai karin bayani…….
A wani labarin kuma, Zan Fara Bai wa Kasashen Afrika Abinci Kyauta Idan Suna Bukata — Shugaba Putin
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yace zai bayar da fifiko wurin ƙarfafa alaka da nahiyar Afirka , a dai dai lokacin da yake kokarin kyautata alaka da ƙasashen waje yayin da yake fuskantar takunkumin da kasashen Yamma suka ƙaƙabawa ƙasar sanadiyar mamaye Ukraime. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Shugaban yace Rasha zata tura abinci zuwa ga kasashen Afirka da ke buƙata kauta idan ba sake dawowa da yarjejeniyar fitar da kayayyakin abinci da aka kulla ba