Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yace zai bayar da fifiko wurin ƙarfafa alaka da nahiyar Afirka , a dai dai lokacin da yake kokarin kyautata alaka da ƙasashen waje yayin da yake fuskantar takunkumin da kasashen Yamma suka ƙaƙabawa ƙasar sanadiyar mamaye Ukraime. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Shugaban yace Rasha zata tura abinci zuwa ga kasashen Afirka da ke buƙata kauta idan ba sake dawowa da yarjejeniyar fitar da kayayyakin abinci da aka kulla ba.
KU KARANTA: Yanzu Lokaci Na ne na zama Shugaban Majalisar Dattawa ta 10 – Kalu
A yan Shekarun nan Rasha na ƙoƙarin faɗaɗa tasirin ta a nahiyar Afirka, yayin Putin yace yayi ammana nahiyar Afirka zata cigaba da fadada ikon ta a fadin duniya.
Wakilai fiye da 40 ne daga kasashen nahiyar Afirka suka hallarci wani taron da kasar ta shirya , kamar yadda Ma’aikatar yaɗa labaran fadar gwamnati Kremlin ta bayyana.
An dai tsara cewa mista Putin zai gana da shugabannin kasashen Afirka a watan Yuni, a taron Rasha da ƙasashen wanda shi ne karo na biyu.
A wani labarin kuma, Mu Taru Mu Dauki Kaddara — Gwamnan Taraba Ya Shawarci APC
Dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben da aka kammala kwanan nan, Sanata Emmanuel Bwacha ya bukaci magoya bayansa da ‘ya’yan jam’iyyar da su amince da abubuwan da rashin faduwarsa zabe domin samun cigaban jihar. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Jalingo, ta hannun Daraktan yada labarai na majalisar yakin neman zaben sa, Aaron Artimas.