Wasu ‘yan bindiga sun bude wa sarakunan gargajiya wuta yayin wani taro a karamar hukumar Njaba na jihar Imo.
Sai dai harkawo hada wannan rahoton ba’a Sami Cikakkun bayanai kan harin ba, Amma haryanzu a na tunanin, akalla sarakunan gargajiya biyar sun mutu yayin harin, tare da raunata wasu da dama.
A wani labarin Kuma na daban.
Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya yi gargadin cewa duk wani dan siyasa da aka samu yana boye ko daukar nauyin ‘yan daba a cikin jihar za a yi maganinsa saboda haka yana mai gargadin cewa gwamnatinsa ba zata lamunci duk wani aikin rashin da’a ba.
Gwamnan ya yi wannan gargadin ne a ranar Litinin a gidan Gwamnati yayin da yake ganawa da shugabannin wata kungiyar ‘yan dabar matasa na siyasa da aka fi sani da ECOMOG.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman kan hulda da jama’a da dabarun yada labarai na gwamnan, Isa Gusau tace Zulum a lokuta daban -daban ya amince da samar da ayyuka da dama da shirye -shiryen karfafawa kungiyoyin don sanya su samun hanyoyin rayuwa na halal.
Sannan yace duk da wadannan matakan, gwamnan ya koka da cewa mafi yawan matasan jihar sun shiga aikin daba a matsayin hanyar rayuwa.
“Borno ita ce kawai wurin da muke dashi, don haka ba za mu iya barin wasu kalilan daga cikin ku su lalata jihar ba. Na yi imani ba ku kadai ne mutanen Borno ba, muna da sama da mutane miliyan shida a jihar. Ba za mu iya ba ku damar ci gaba da tsoratar da jama’a ba, ba za mu iya yin haƙuri da hakan ba. ”
Kazalika “Ba za mu ci gaba da baku kuɗi ba, ba za ku iya riƙe mu don fansa ba. An umarci hukumomin tsaro dasu yi maganin duk wanda aka samu yana nuna kansa a matsayin ECOMOG, ko a filin jirgin sama, makabarta, liyafar aure ko a ko’ina.Kun kasance kuna hargitsa zaman lafiyar jama’a, kuma kuna haifar da tashin hankali “a cikin jihar,a cewar sanarwar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “idan zaku iya tunawa a watan Yulin shekarar 2019, wanda ya kasance watanni biyu bayan hawan sa mulki, Gwamna Zulum ya bada sanarwar hana yin dabar siyasa a Maiduguri, wanda a tsakiyar 2000s, ya fuskanci rikici na jini tsakanin ‘yan bangar siyasa da suka hada da kashe -kashe. Ya kaddamar da shirin samar da sana’o’in hannu domin tallafawa matasa.