Yannbindiga sun yi garkuwa da wani sabon jami’in ‘yan sanda dake kula da reshen Birnin Gwari a jihar Kaduna wato DPO.
An sace DPO din ne a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da misalin karfe 9 na safe a ranar Litinin.
Majiyoyi sun shaida wa jarodar Daily Trust cewa DPO din na kan hanyarsa ta zuwa Birnin Gwari ne domin kai rahoto a bakin aikinsa lokacin da aka sace shi.
Ba a bayyana ko jami’in na tafiya shi kadai a cikin motar lokacin da aka dauke shi ba.
Har yanzu dai ‘yan sanda ba su mayar da martani ko kuma fitar da wata sanarwa a hukumance kan sace jami’in ba.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalinge, ya ce, “zan binciki labarin faruwar lamarin kuma in dawo gare ku nan ba da jima wa ba”
A wani labarin kuma.
Wasu ‘yan bindiga sun sace mutane uku, sun bukaci a biya su N40m a jihar Kogi
Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da mutane uku a yankin Ayere na jihar Kogi yayin da suke tafiya wani gari kusa da Ibaram zuwa Akoko a jihar Ondo.
An yi zargin cewa wadanda aka yi garkuwa da su, sun tafi wani taron jama’a ne a Ibaram lokacin da aka sace su.
Bayan an kai wa motarsu hari, masu garkuwa da mutane sun kama su tare da yin garkuwa da su a dajin
Da yake magana game da lamarin, wani dan uwan daya daga cikin wadanda abin ya shafa ya bayyana cewa tuni masu garkuwa da mutanen suka sanya kudi naira miliyan 40 a matsayin kudin fansa kuma ana ci gaba da tattaunawa don ganin an rage masu.
Lamarin dai ya faru ne a jihar Kogi, wanda rundunar ‘yan sandan Ondo ta yi ikirarin cewa yankin ba a karkashin kulawarsu yake baba lokacin da aka tuntube su.
Bayan wannan lamari, Akala na Ikaram, Oba Andrew Momodu, ya gargadi matafiya da ke kan titin Ajowa/Ayere/Kabba da Ikaram Akunu zuwa Ayere da su yi taka tsantsan tare da guje wa tafiye-tafiye da daddare domin akwai masu aikata laifuka da yawa a dazuzzukan.
Oba Momodu ya bukaci jami’an tsaro, ’yan banga, da mafarauta ’yan asalin jihohin biyu da su hada kai don dakile miyagun laifuka, musamman sace-sacen jama’a, wanda ya ce ya zama ruwan dare gama gari.