Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kaduna, KADSEMA, ta ce za ta bayar da tallafi ga gidaje 231 dake yankuna 10 da ‘yan bindiga suka raba da gidajensu a karamar hukumar Kachia.
Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari ga al’ummomi a karamar hukumar a ranar 23 ga watan Yuni, inda suka kori mutanen daga gidajensu.
Mista Muhammed Mukaddas, babban sakataren hukumar ya shaidawa NAN a yau Litinin a Kaduna cewa hukumar ta kammala tantance al’ummomin da abin ya shafa domin tallafa musu.
Shugaban hukumar ta SEMA ya ce an gudanar da tantancewar ne tare da hadin gwiwar kungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya da kwamitin bayar da agajin gaggawa na karamar hukumar Kachia.
Ya lissafa al’ummomin da abin ya shafa da cewa sun hadar da Pachi, Kabode, Insime, Yelwa Gora, Rumuda, Kasan Kogi, Karmai, Maiido Kufai, da Rafi.
Mukaddas ya ce an samar wa ‘yan gudun hijira mafaka na wucin gadi a makarantun firamare daban-daban na Kachia.
Ya ce jami’an tsaro suna bakin kokarinsu wajen ganin an dawo da zaman lafiya a tsakanin al’umma.