Gwamnatin jihar Borno ta rufe hedikwatar jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) na jihar da ke Maiduguri babban birnin jihar.
Daily Trust ta ruwaito cewa, an ta rufe hedikwatar jam’iyyar tare da wasu ofisoshinta a ranar Alhamis.
Dan takarar gwamnan jihar Borno a karkashin jam’iyyar NNPP, Dakta Umaru Alkali, ya tabbatar da haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri.
Ya kara da cewa an kama dan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar na Borno ta tsakiya, Hon Attom Muhammad Maigira, bayan da ya amsa gayyatar ‘yan sanda.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-duminsa: NAAT Ta Dakatar Da Yajin Aikin Watanni 3
Ya ce an tura ‘yan sandan zuwa Sakatariyar Jam’iyyar da ke kusa da Abbaganaram da Gidan Maradara tsakanin Laraba zuwa Alhamis domin hana ‘yan jam’iyyar shiga ofishinsu.
Wakilin Majiyar Dimokuradiyya da ya ziyarci mahadar Abbagannaram da misalin karfe 11:30 na safe ya ce, ya ga an ajiye dimbin jami’an ‘yan sandan kwantar da tarzoma tare da motocin sintiri a wurin.