– An bayar da rahoton cewa wata ma’aikaciyar jinya wacce ta ɗauke tsammanin kasancewar ta uwa ta yi maraba da jaririnta tana da shekaru 71 da haihuwa.
– Matar ta yi farin ciki matuka a lokacin da take nuna lafiyar jaririnta, inda ta ce ta haihu ba tare da wata matsala ba kuma cikin mintuna 10.
– Yayar mahaifiyar ta ce aunty ta yi aure tana da shekara 50 kuma ta jira shekara 21 kafin ta haifi danta.
Wata tsohuwa ‘yar shekara 71 a Najeriya na cikin wani yanayi na murna bayan da ta yi maraba da jaririn ta bayan shekaru 21 da aure.
Uzo Oge, yayar mai jegon, ta ziyarci matar a gidanta da ke Fatakwal tare da mahaifiyarta don yi musu albishir.
Da take naɗar ziyarar ta wayarta, Oge ta bayyana a wani faifan bidiyo na TikTok cewa kakarta ta yi aure tana da shekara 50 kuma ta ɗauke duk wani tsammanin haihuwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wata dattijuwa ‘yar shekara 54 ta haifi ya’ya uku.
Mai jegon cikin zumuɗi ta kasa danne farin cikinta, hakan yasa sai da ta godewa Allah.
Sakonni da majiyarmu ta aikewa Oge ta TikTok don tabbatar da labarin da ta wallafa ba a amsa ba har zuwa lokacin da ake wallafa wannan rahoto.
Ga wasu daga cikin ra’ayoyin waɗan da suka bibiyi wannan labarin suka bayyanawa majiyarmu.
@WONDER ya ce: “Ina baban yake, shi nake san gani domin naga irin ƙarfinsa. “Na gode.”
@chiichii <3 ta ce: “Chaii wannan ya zubar min da hawaye! Ai babu abin da Allah ba zai iya tafiyar da shi ne ba.
@Eli Tan ya ce: “Na gode Allah kuma na taya Mama murna, Allah ba ya neman izni ga kowa. Allah ya sa miki albarka.”
Wonder ta ce: “Alhamdu lillahi uwar gida ina fatan ki yi tsahon kwana, domin ki kula da jaririnki. Duk iyaye ina yi musu fatan tsahon kwana dan su kula da ‘ya’yansu m.”
@Virtue Michael ya ce: “Ba wani abu da Allah ba zai iya yi ba, na gode masa har abada, tabbas zai yi mini nan ba da jimawa ba, na gaskata Shi.”