Jiga-jigan jam’iyar APC Mai Mulki a jihar Zamfara, sun fito fili sun nuna rashin amincewar su kara-ra, bisa ai wa gwamnan jihar Bello Matawalle mukamin Shugaban cin jam’iyar a jihar, da Mai Mala Buni ya yi.
Jiga-jigan da su ka hada da Tsohon Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, Sanata Kabiru Marafa, da tawagar su, sun bayyana hakan ne jim kadan bayan ganawar da su kayi da Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-rufa’i a jiya Alhamis, a garin Kaduna.
Inda a bayan taron ne a kaji, tsohon Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz ya ri na cewa, “Babu wanda ya Isa ya rusa jagorancin jam’iyar jihar, a lokaci guda” inji shi.
Inda ya kara da ce,” Mun yi wata ganawa da gwamnan Mai Mala Buni da wasu Gwamnonin, amma akan sharadin cewa, zamu je ne kawai mu kaddamar da shigowar Matawalle jam’iyar APC, inda daga bisani kuma Buni ke ai ya na shi amastayin Shugaban jam’iyar a jihar Zamfara, Wanda mu kuma bamu aminta da hakan ba.” Inji Yari.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nafara samun Nasara inji Mariya Ibrahim
A nashi bangaren Sanata Kabiru Marafa, ya ce, Sam wannan maganar ba mai yiwuwa bace, kuma sake zaman tattaunawa ce kadai, zata magance dukkan matsalolin.
Shi kuwa anashi jawabin gwamnan jihar Kaduna cewa ya yi, Gwamnonin jam’iyar ta APC, “Za mu shirya wani zama na musamman ko a jihar Kaduna, birnin tarayya Abuja, ko kuma a garin Gusau da ke jihar Zamfara, wanda ake saran hakan zai magance matsalar da ke tsakanin bangarorin biyu.” Inji El-rufa’i
Idan za’a iya tunawa dai, A ranar Talatar da tagaba ta ce, Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya sauya sheka daga jam’iyar adawa ta PDP, zuwa Jam’iyar APC nai Mulki, inda a nan ne Kuma, Shugaban kwamitin gudanarwar Jam’iyar na Kasa, kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya bai wa Matawalle jagorancin jam’iyar APC a jihar, wanda haka ne ya yi sanadiyar kawo ce-ce ku-ce tsakanin bangarorin biyu.