Na fara samun nasara a harkar fim
Mariya Ibrahim (Sister Atine)
Daga Mukhtar Yakubu Kano
Duk wanda ya ke kallon shirin Dadin Kowa, na Arewa 24 ba zai manta da Sister Atine ba, wato likitan da ta yi suna a wajen rashin tausayin mara lafiya, don haka ne ma a ke yi mata kallon mara tausayi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar soji ta kama wani da ake zargin Dan kungiyar ISWAP
Sai dai kuma a na ta bangaren Mariya Ibrahim, ta bayyana wa wakilin mu cewar, ita wannan shirin na Dadin Kowa shi ne ya fito da ita, har ma ta ke ganin ta kama hanyar cin nasarar da ta ke su ta samu a cikin masana’antar.
Domin kuwa a zantawar da su ka yi da wakilin mu, ta bayyana cewar, “Gaskiya harkar fim Allah ya sa zan shiga cikin ta, domin bayan mutuwar aure na, na shigo ina yin fina-finai kadan-kadan, kuma daga baya Allah ya sa na samu kaina a Shirin Dadin Kowa, wanda kuma da shi ne Allah ya sa mutane suka sanni a duniya, amma dai, na san na fara shiga harkar fim ne a shekarar 2018. Don haka kafin Dadin Kowa na yi ta kokarin na samu shiga harkar, wadda zan zamo babbar Jaruma kamar yadda na ke da buri a zuciya ta, amma har sai da ta kai na fara hakura da tunanin zan zama wata a cikin harkar fim, don haka ma na ke ganin a lokacin ba zan samu damar kaiwa wajen da na ke son kai wa ba, saboda babu wanda ya sanni, kuma ina yin harkar fim din amma yanzu kuwa Alhamdulillah, na fara hango nasara, tun da a yanzu duk in da na shiga, da wuya a ce babu wanda ya sanni a wajen, don sai ka ji ana cewa ga masifaffiyar likitar Dadin Kowa, ko kuma a ce ga Sister Atine. Gaskiya ina jin dadin hakan, don sai na ji kamar ba ni ba ce, saboda haka ina godiya ga Allah da ya kai ni ga samun wannan nasarar. ”
Daga karshe ta yi kira ga masu kallon ta a fim, da su sani abin da ta ke yi a cikin shirin Dadin Kowa ba halin ta ba ne, ya nayin aikin ne ya zo da haka.
Comments 3