Daga Mukhtar Yakubu.
A wannan rana ta Asabar 31 ga watan Yuli shekarar nan ta 2021, wasu daga cikin yan fim da mawaka, suka tsara za su gudanar da wata zanga-zangar lumana, domin nuna fishin su ga kafar yada labarai ta Sahara Reporters, dangane da labarin da ta buga wanda a ke ganin taba darajar Manzon Allah S.A W.
Kamar yadda daya daga cikin jagororin Zanga-Zangar Abdullahi Amdaz, wanda akafi sani da Excellency ya sanar, inda ya ce, za su fara zanga-zangar ne da misali karfe daya na rana, wanda kuma za su hadu ne a Gidan Dan Asabe da ke titin zuwa Gidan Zoo, kuma daga nan za su dunguma zuwa fadar Gwamnatin Kano, domin su kai kukan su, da kuma nuna bacin ran su, dangane da abin da jaridar ta rubuta.
A kan haka ne su ke gayyatar dukkan masu gudanar da harkokin sana’ar su, a cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood, da ‘yan Jarida, da kuma sauran jama’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Fitacciyar Jaruma Rachael Oniga ta rasu
Take zanga-zangar dai shi ne, ‘Ba mu yarda da cin zarafin Manzon Allah ba” Kuma za a tafi ana dauke da kwalaye, masu dauke da rubutun #Say No to Sahara Reporters.
#We Love Our Prophet Muhammad.
#We Wan Action.
Abdullahi Amdaz ne, da Umar Nuhu Abba, Umarkhan, za su jagoranci zanga-zangar ta lumana da za a gudanar a yau din.
A wani labarin Kuma na daban….
Yanzu-Yanzu: Fitacciyar Jaruma Rachael Oniga ta Rasu
Rahotanni sun bayyana cewa, shahararriyar Jaruma a masana’antar fina-finai na Kudancin Nigeria wato Nollywood, mai suna Rachael Oniga ta rasu.
Dan ta mai suna Olatunji ne, ya tabbatar wa manema labarai mutuwar ta, a yau Asabar.
Acewar shi, mahaifiyar ta shi, ta mutu ne da musalin karfe goma na daren jiya juma’a.
Kafin mutuwar Margayiya Oniga, ta sha fito a ciki wasu fina-finai masu, a Masana’antar Nollywood na turanci, da kuma na kabilar Yarbawa.
An haife ta ne a ranar 23 ga watan Mayun shekarar 1957, inda ta fara fito wa a matsayin Jaruma a shekarar 1993, da ta fito a cikin fim Mai sunan Blockbuster da kuma Onowe da aka yi shi da yaran Yarbanci.
Tsohuwar jarumar Mai shekarar 64, ta yi aiki da wani kamfanin Injiniyancin na kasar Habasha, dake da Babban ofishi a Nigeria.
A wani hira da aka yi da ita kafin rasuwar ta ta ce, ta dai-na aiki da kamfanin bayan tayi aure domin tafara tara iyali, sai dai auren na ta bai jima ba, ta fito.
Bayan rabuwar ta da mijin ya’yan na ta, sai kuma ta koma taka rawa a Masana’antar fina-finai na Nollywood.
Kazalika ta sha fadi a tattaunawar ta da mane ma labarai kafin rasuwarna ta cewa, babban danasani da ta yi a rayu shine, rashin tsawa na neman hakkin ta na aure, bayan rabuwar ta, da mijin na ta.
Comments 1