Kwanaki 34 bayan da Gwamnatin Tarayya ta umarci kamfanonin sadarwa da su hana masu amfani da layin waya (SIM) wanda ba a hada shi da Lambobin Shaidar katin dan Kasa ta NIN ba, yanzu haka adadin wadanda suka shiga cikin kundin Hukumar Samar da katin dan kasar sun karu sosai.
Hukumar Kula da bayar da katin dan kasar (NIMC) ta ce sama da miliyan 82.73 ne suka karu kan wadanda suka samu katin a baya sakamakon yadda aka dakatar da layukan su daga kiran waya.
A ranar 4 ga watan Afrilu ne dai gwamnatin tarayya ta umurci kamfanonin sadarwa, ta hanyar Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), da su hana sama da layukan waya miliyan 72 kira sakamakon kin hada NIN din su da layin wayar.
Dangane da bayanan da aka samu daga kundin rajistar hukumar a watan na Mayu 2022 dake Internet ya kai sama da miliyan 82.73.
Jihohin dake kan gaba wajen yawan masu samun lambar NIN din sun haɗar da jihar Legas mafi yawan adadin masu rajista sama da miliyan 9.48.
Yayin da bayanan, bisa ga jinsi, ya nuna cewa maza 46,564,578, ne suka yi rijistar, sai kuma mata sun kasance 36,173,574.