By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘ya’ya mata biyu na tsohon kwamishinan hukumar NPC, Zakari Umaru-Kigbu da aka kashe kwanan nan sun samu ‘yanci daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.
A ranar Lahadin da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki gidan Umar-Kigbu da ke garin Azuba Bashayi a karamar hukumar Lafiya ta jihar Nasarawa inda suka yi awon gaba da ‘ya’yansa bayan sun kashe shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Jami’in Dan Sanda Ya Shiga Tsaka Maiwuya Biyo Bayan Shararawa Wasu Fararen Hula 2 Mari A Ilori
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, ASP Ramhan Nansel, a ranar Laraba ya tabbatar da sakin su ga Jaridar Daily Trust ta wayar tarho.
Ya ce an kubutar da yaran ne sakamakon matsin lamba da masu garkuwa da mutane suka sha a kusa da wani dutse da ke karamar hukumar Nasarawa Eggon a jihar.
Ya ce an dawo da wadanda abin ya shafa da iyalansu bayan an duba lafiyarsu a asibitin kwararru na Dalhatu Araf. Da aka tambaye shi ko an biya kudin fansa domin a sake su, PPRO ya ce rundunar ba ta da masaniya kan haka.
Sai dai wata majiya mai tushe ta ce an biya kudin fansa Naira miliyan 30 ga masu garkuwa da mutanen kafin a sako yaran.