Ministar Muhalli, Sharon Ikeazor, ta ce nan ba da dadewa ba ma’aikatar za ta fara bayyana suna tare da tozarta Ma’aikatu da cibiyoyi da suka kasa daidaita ban dakunan su.
Ta ce hakan ne dai zai taimaka domin kawo karshen bahaya a fili a fadin kasar nan.
Ta yi wannan jawabi ne a Abuja ranar Litinin a wajen bikin cika shekaru biyu da kafa gaggamin wayar da kan al’uma na ‘Clean Nigeria: Use the Toilet’ wanda ma’aikatun muhalli da albarkatun ruwa suka shirya tare.
Ministar wacce ta samu wakilcin babban sakatare a ma’aikatar, Hassan Musa ya ce: “Shugaban kasa ya ba da umarni dole ne jami’an kula da muhalli na tarayya, jiha da kananan hukumomi, suyi yin aiki tare domin magance matsalar.
“Ma’aikatar za ta inganta tsarin sa ido, tare da ziyartar wurare daban-daban, Kuma duk Lokacin da muka ziyarci wasu wurare, za mu fallasa su ga duniya. Watakila hakan zai iya sa ‘yan Najeriya su tashi zaune.
“Dole ne a amince da dukkan gine-gine a Najeriya gami da adadin bandakuna. Yayin da ake kan amincewa, kuma ana buƙatar la’akari da wuraren banɗaki. Idan aka kammala ginin ma’aikatan lafiya suma suna bukatar duba kayan bayan gida.”
Anashi bangaren Ministan Albarkatun Ruwa, Suleiman Adamu, ya bayyana cewa a cikin kimanin mutane miliyan 494 da ke yin bahaya a fili a duniya, miliyan 46 ‘yan Najeriya ne.
Ya ce wannan ya sanya Najeriya a cikin kasashen da ke da yawan mutanen da ke da hannu a cikin lamarin.