Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya isa garin Jos Babban Birnin jihar Filato, domin wani taro da kungiyar Pentecostal Fellowship of Nigeria ta shirya wanda gwamnan Filato Simon Lalong ya tarbe shi.
Gwamnatin jihar ce ta bayyana hakan a shafin ta na Facebook a ranar Asabar a wata sanarwa mai taken, ‘Gwamna Lalong ya karbi bakuncin mataimakin shugaban kasa Osinbajo a Jos’.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Mataimakin shugaban kasar da ya sauka a filin jirgin sama na Yakubu Gowon Heipang ya samu tarba daga gwamna Simon Bako Lalong na jihar Filato.
“Haka nan a filin jirgin sama domin tarbar mataimakin shugaban kasa akwai mataimakin gwamna, Sonni Tyoden; Kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Yakubu Sanda; Babban Alkali Yakubu Gyang Dakwak; da sauran manyan jami’an gwamnati.”inji sanarwar.