Yunƙurin Shirin Pulaaku na Tallafawa Magance Matsalar tsaro a Arewa ya samu sahhalewar Shugaba Tinubu
Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima ya ce shugaba Bola Tinubu ya amince da shirin “Pulaaku Initiative”
Pulaaku ba shi ne ke da alhakin magance matsalar tsaro da tashe-tashen hankula daga ‘yan bindiga a Arewa ba, amma kuma a cewar Mataimakin Shugaban ƙasar, Tinubu ya ware Naira biliyan 50 ga shirin tun a karon farkon.
Shettima ya bayyana hakan ne a Jawabin sa na bude taron yini biyu kan rashin tsaro a Arewacin Najeriya da kungiyar hadin kan Arewacin Najeriya ta shirya mai taken “Yin Amfani da maban-bantan hanyoyi wajen magance Matsalar tsaro a Arewa” wato “Multi Dimensional Approach to Tickling Tacking Insecurity in Northern Nigeria”.
Tsohon Gwamnan Borno wanda Shugaban Ma’aikatan sa Ibrahim Hadeija ya wakilta ya ce, shirin da aka amince da shi a yanzu zai fara ne a Jihohi biyar na Arewa wato Jihohin Sokoto, da Kebbi, da Katsina, da Benue, da Zamfara, da Niger da kuma Kaduna, wanda a cewar sa hakan kuma zai “kawo” yalwatuwar arzikin yankin Arewa.
KARANTA WANNAN LABARIN:Sojoji sun yi nasarar hallaka Ƴan bindiga uku Tare Da kwace Muggan Makamai a Taraba
Kowane yanki na kasar yana daidai da sauran, kuma Gwamnati na ɗaukar bukatun kowane yanki a matsayin mai mahimmanci.
Ga Arewa mu ma muna tafe da yunƙurin kawo sauyi don magance tushen ƙalubalen da ake fuskanta na rashin tsaro.
Kungiyar Pulaaku Initiative mai zaman kanta ta samu amincewar Shugaban kasa tare da ware mata Naira Biliyan 50 a matakin farko domin soma gudanar da shirin ta.
Wannan shiri na da nufin inganta rayuwar zababbun Jihohin da suka haɗa da Sokoto Kebbi Katsina Benue Zamfara Niger da kuma Kaduna.
Baya ga haka, yunƙurin Gina makarantu, da Tituna da sauran muhimman ababen more rayuwa na cikin shirrin ne don cika alƙawarin samar da wadataccen arzikin wannan yankin da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka,” in ji shi.
Shettima ya bayyana cewa Gwamnati ta dukufa wajen magance matsalar rashin tsaro a kasar nan baki ɗaya.