Gwamnan Jahar Edo Mr Godwin Obaseki a ranar Talata, yayi kira ga masu zaɓe a Jahar Anambra, dasu nemar wa jahar makoma ta gari, ta hanyar zaɓar PDP da Ɗan takarar ta Dr. Valentine Ozigbo a zaɓen Gwamnan jihar na ranar Asabar a Jahar.
Obaseki yayi wannan kiran a lokacin da yake jawabi ga ƴaƴan Jami’iyyar, a filin taro na Ekwueme dake Awka Jahar Anambara, a lokacin gangamin yaƙin neman zaɓe, gabanin zaɓen Gwamnan Jahar.

KARANTA WANNAN LABARIN: Nnamdi Kanu yafi zaɓen Anambra mahimmanci, ku sake shi domin a samu zaman lafiya — Cewar Doyin Okupe
Obaseki wanda ya samu wakilcin Mataimakin sa Kwamared Philip Shaibu, ya buƙaci masu zaɓe, dasu zaɓi Ɗan takarar PDP da mataimakin sa, inda yace suna ƙudirin kawo canji a Jahar.
“Kada kuji tsoron fitowa da yawan ku a ranar Asabar tare da yin zaɓe, da gudun zaɓen ƴan siyasa da suka yi ritaya, kuma basu da wani abun kirki da zasu kawo wa jahar. Mutumen da zaku zaɓa a ranar Asabar shine Dr. Ozigbo, kuma jamiyyar da zaku zaɓa itace PDP.”
A jawabin shi, Gwamnan Jahar Delta Sanata Ifeanyi Okowa yace samun nasarar zaɓen jamiyyar PDP wata manuniya ta ƙudirin jam’iyyar na ceto Najeriya.
Comments 1