Zaɓen 2023: Tambuwal ya rasa wani hadimin sa ga APC
Alhaji Abubakar Kwaire, mai ba Gwamna Aminu Tambuwal shawara na musamman ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) gabanin zaben 2023 a jihar.
Kwaire, a cewar wata sanarwa da Bashar Abubakar, mai baiwa Sanata Aliyu Wamakko, shawara ta musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a ya fitar, ya samu tarba daga dan takarar gwamnan jihar na APC, Alhaji Ahmad Aliyu a Sokoto.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ana Tsaka Da Rashin Kudi A Hannu, SERAP Ta Maka Majalisun Kasa Kotu
Kwaire ya yanke shawarar komawa APC, a cewarsa, halayen shugabancin Wamakko ne suka sa shi.
“Saboda haka, na yi imani da Wamakko a matsayin shugaban jam’iyyar APC da kuma Aliyu za mu gudanar da mulkin jiharmu, idan aka zabe shi, ana sa ran samun ribar dimokuradiyya,” inji shi.
A nasa jawabin, dan takarar gwamnan ya yi maraba da wanda ya sauya sheka tare da ba shi tabbacin za a yi masa daidai da sauran ‘ya’yan jam’iyyar.
Kwaire wanda tsohon dan majalisar dokokin jihar Sokoto ya fito daga karamar hukumar Tambuwal.
A wani labarin kuma:Kwanaki bakwai ya yi yawa– Wani Sanata ya yi tsokaci ga Buhari kan ƙarancin takardun kuɗi
Wani dan majalisar wakilai na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Sanata Smart Adeyemi na jihar Kogi, ya ce kwanaki bakwai ya yi yawa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari domin magance matsalar karancin kuɗi
Adeyemi, tsohon shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja.