Zaɓen Fidda Gwani na Lagos: Kyarma na nan na Jiran ka ranar Lahadi a Abuja— Kperogi ya caccaki Tinubu
Sanannen Marubucin nan , kuma mai sukar Gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Farooq Kperogi ya caccaki Jigon Jam’iyyar APC na Ƙasa Asiwaju Bola Tinubu akan sakamakon Zaben Fidda Gwani na Gwamna.
Gwamna Babajide Sanwa-Olu wanda ya Tinubu ya amince ya nemi wa’adi na biyu, ya samu Tikitin Jam’iyyar bayan Zaɓen Fidda Gwani da akayi, wanda ya faru da rikici daya haddasa cire ƴan takara biyu da suke ƙalubalantar Sanwa-Olu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Ɗuminsa: Tsohon Shugaban Sojojin Sama Saddique ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani na Jam’iyyar APC a Bauchi
Adamu Yuguda Shugaban Kwamitin zaɓen, bayan ya cire ƴab Takarar, yace Gwamna maici shine ya samu nasarar lashe zaben.
Mr Yuguda yace “muna sane da cewa ƴan Takara guda 3 suka yi Fom na Tikitin Gwamna a Jahar Lagos. An tantance mutum 1, to shi kaɗai zamu kalla, tunda shi kaɗai Uwar Jam’iyya ta tantance,”.
Amma da yake maida jawabi, daya daga cikin ƴan Takarar Oluwa ya zargi Kwamitin da yin amfani da wasu ƴan Siyasa domin murɗe zaɓen.
Lamarin hana ƴan Takara zuwa Filin taron, na ɗaya daga cikin abinda ya haifar da zazzafar muhawara a ranar Alhamis.
Da yake maida jawabi a shafin sa na Facebook, Kperogi yace Kyarma na nan na jiran Tinubu a zaɓen Shugaban Ƙasa wanda zai fara a ranar Lahadi.
Comments 1