Ministan Ƙwadago De Chris Ngige yace zai bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar Shugaban Ƙasa a watan Afrilu.
Ngige, ya bayyana haka a Awka Babban birnin Jahar Anambra, a lokacin rarraba kayayyakin tallafi ga wasu da suka kammala ɗaukar horo masu karatun digiri a Jahar.
Wasu da suka amfana sun tambayi Ngige daya nemi takarar shugaban Ƙasa a shekarar 2023 ba tare da ɓata lokaci ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: DCP Abba Kyari ya goge dukkanin rubuce-rubucen shi a Facebook, bayan ya ɗora hotuna 462 na ɗan gidan IG na Ƴan sanda
Dasuke bayyana tsohon Gwamnan Jahar Anambra a matsayin mutumen mutane, wanda ya nuna ƙwarewar sa a iya mulki, waɗanda suka amfana wanda yawancin su mata, sun ce ya cancanta ya maye gurbin.
Dayake maida jawabi, Ngige yace lokacin daya ɗiba na neman shawarwari bai ƙare ba, ya kuma buƙaci mutane su bashi lokaci har zuwa lokuttan bukukuwan Easter.
A cewar Ngige yace bada tallafin kashi II na biyu ne, domin tallafawa mutane su cigaba da kasuwanci.
Comments 1