Zaɓen Shuwagabannin APC: Wata Ƙungiya ta goyi bayan sabon Shugaban Kwamitin Ruƙo Abubakar Sani
Wata ƙungiya mai rajin cigaban Jam’iyyar APC ta Jahar Akwa Ibom ta bayyana goyon bayan ta ga Shugaban Kwamitin Ruƙo na Jam’iyyar APC na Kasa.
Shugaban Dattawan Ƙungiyar a Jahar, kuma Tsohon Gwamnan Jahar Ogun, Sam Ewang yace Jahar tana bayan Mulkin Abubakar Sani Bello.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 6 Sun Mutu, 16 Sun Jikkata A Wani Hatsarin Babbar Motar Dakon Kaya A Jihar Edo
“A madadin Shugaban Ƙungiyar Dattawan Jam’iyyar APC, Ina Taya Shugaban Kwamitin Ruƙo wanda kuma shine Gwamnan Jahar Niger Abubakar Sani Bello. Akwa Ibom tana goyon bayan abinda kake yi. Muna murna, kuma ka cigaba.
“Mun amince da tsarin karɓa-karɓa na shiyyoyi na Jam’iyyar. A matsayin mu na Dattawa a Jahar Akwa Ibom, muna Son zuwa Abuja domin haɗuwa da Kwamitin ka,” inji shi.