By Abbas Yakubu Yaura
A jiya ne aka kashe mutane hudu tare da jikkata wasu da dama a yankin Ahentse da ke Ndzorov a karamar hukumar Guma ta jihar Benue.
Garin na Ndzorov wanda ya kasance shine gidan kakanni na Gwamna Samuel Ortom.
An ce maharan sun shiga kauyen ne ta cikin kauyen Damkor inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.
An kashe mutane hudu yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka a yayin harin.
Wani dan unguwar da ya tsallake rijiya da baya, Daniel Gwa, ya shaidawa jaridar The Nation cewa, harin ya afku ne kusa da rundunar sojojin da ke da tazarar kilomita 5 daga wurin, amma har yanzu babu wani martani daga jami’an tsaro.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kate Anene ta tabbatar da harin.
Jihar ta Benue dai a ‘yan kwanakinnan tana fama da mtsalar yawan samun rikicin makiyaya a tsakanin al’umomin dake jihar.
Lamarin dai na rikicin makiyaya yana ciwa mahukunta tuwo a Kwara inda su ke yin duk mai yiwuwa wajen ganin sun dakile irin wadannan tashe tashen hankula tsawon shekaru