Hukumar kula da ilimin kimiyya da fasaha ta kasa (NBTE) a ranar Litinin din nan ta bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a dauki ma’aikatan da suka mallaki matakin ilimi na Higher National Diploma (HND) aiki a matsayin Mataimakin Malaman Makarantun Kimiyya da Fasaha da Monotechnics wato mataimakan Lakcarori.
Sakataren zartarwa na hukumar Farfesa Idris Bugaje ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Kamfanin dillancin labara Kasa a Kaduna.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa Bugaje ya yi nuni da cewa a halin yanzu masu digiri ne kadai ake daukar aiki a kwalejin kimiyya da fasaha a matsayin mataimakan malamai.
KU KARANTA KUMA Hukumar NBTE Ta Gano Wasu Haramtattun Cibiyoyin Kimiyya
Ya koka da yadda aka mayar da masu HND a matsayin masu kimiyya da fasaha a dakunan gwaje-gwaje da kuma bita a bangaren fasaha na makarantun polytechnic, wanda ya bayyana a matsayin “babban rashin adalci”.
“Don me wani daga jami’a zai zo ya yi babakere a kan wani tsari na daban ya zama shugaba a kansu?”
“Mafi girman matsayi a cikin kwalejin fasaha shine HND, saboda haka, mafi kyawun waɗannan waɗanda suka kammala karatun ya kamata a ɗauke su aiki a matsayin mataimakan malamai kuma su girma a cikin tsarin don samun digiri na biyu.”
“Za su iya tasowa ta hanyar matsayi don zama manyan malamai kuma a ƙarshe su zama shugabanni na cibiyoyinsu.”
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Shugaban NBTE ya ce yanayin zai canza tare da sabon tsarin aiki na sashen koyar da fasaha da koyar da sana’a (TVET).
A Wani Labarin Kuma IGP Ya Umarnin Kafa Kwamitocin Zabe Tsakanin Hukumomin Tsaro
Babban Sufeto Janar na ’yan sanda kasar nan, Mista Usman Baba ya umarci kwamishinonin ‘yan sanda a duk fadin kasar nan da su fara aiki da kwamitocin tuntuba tsakanin hukumomin da ke kula da harkokin zabe.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar , CSP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.