Kamar yadda maza suke zagewa su buga wasan gasar ƙwallon ƙafa haka suma mata suke dagewa su buga wasan inda wani lokacin ma har sunfi wasu mazan iya taka leda. Hakance ta sanya yanzu mata suka dage sosai da sosai suke bayar da gudun mawa yadda ya kamata.
A wanan rana ta Lahadi za a baiwa ‘yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ɓangaren mata kofi wanda itace ta zamo zakara, za a bata kofin mai taken League Champion na kakar wasa ta 2019 zuwa 2020 kenan biyo bayan zamowa zakara datayi.
Za a bata wannan kofi ne da rana bayan sun tashi daga wasan da zasu fafata da ƙungiyar ƙwallon ƙafan mata ta EDF Logrono inda za a fafata wasan a birnin Catalonia na ƙasar ta Andalus kuma a filin da aka gudanar da wasan na wannan rana ta Lahadi.
Haka idan ba a manta ba koda a ɓangaren mata akwai ƙungiyar ƙwallon ƙafan da tafi yawan lashe gasar zakarun ƙwallon ƙafa ta mata ta nahiyar turai wato ƙungiyar ƙwallon ƙafan mata ta Lyon dake ƙasar Faransa wadda itace ta zamo jigo a nahiyar ta turai kuma sunanta ya baza duniya wajen yawan lashe gasar, hakan ta faru ne bayan gogaggun ‘yan wasa da suke dasu a duniyar ƙwallon ƙafa.
A shekarun baya ma akwai ‘yar wasa mace wadda ta bayyana cewar idan da dama a barta ta koma cikin maza ta fafata wasan ta inda taso ta koma ƙungiyar ƙwallon ƙafan maza ta Fernabache dake ƙasar Turkey, wannan ‘yar wasa ba wata bace face shahararriyar ‘yar wasan nan ta ƙasar Brazil wato Marta.