Oladipo Olasope, dan tsohon Dan Jaridar nan na gidan Talabijin mai suna Kunle Olasope, ya ce za a binne mahaifinsa da lasifika (microphone) wanda za a sanya lasifikan a cikin akwatin gawarsa.
Dan Marigayin Olasope, wanda Lauya ne da ya kai matakin SAN, ya bayyana hakan ne ga manema labarai a garin Ibadan a ranar Juma’a.
Marigayin ya rasu ne a ranar 6 ga watan Oktoban yana da shekara 82 a garin Ibadan bayan ya yi fama da gajeren rashin lafiya.
Marigayin shi ne namiji na farko da ya kasance ma’aikaci a tsohin gidan Talabijin na WNT wanda aka kafa a garin Ibadan a karkashin shugabancin yanki na Cif Obafemi Awolowo.