Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Thomas Partey ka iya fuskantar hukunci mai tsanani bisa karye dokar bada tazara ta korona bayan da aka ganshi yana rawa a wani gidan rawa a daren jiya litinin.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafin Instagram ya nuna dan wasan mai tsadar Yuro miliyan 45 har da wani sabon salon rawa wurarne karfe uku na dare.
Dan wasan mai shekara 27 dan kasar Ghana ya kuma fito cikin wani salo da magoya baya wanda ake gani ciki har da budurwarsa na chashewa yan sa’o’i bayan da kungiyarsa ta Arsenal ta karkare gasar Firimiya cikin wani mawuyacin hali.
Da ma dai kasar Birtaniya ta haramta bude gdajen rawa a wani matakin kare kai daga cutar nan ta Korona inda ta ce karye doka ne a samu wani a gidan rawa.