Wata kotu a ƙasar Uganda ta yankewa wani matashi hukuncin kisa bayan samunsa da laifin aikata luwaɗi a ƙasar.
Lauyansa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, matashin mai shekara 20 shine na farko da za a yankewa wannan hukuncin tun bayan da majalisar dokokin ƙasar ta rattaba hannu kan dokar haramta luwaɗi a watan Yuni.
Ana zargin matashin ne da tirsasawa wani mutum mai shekara 41 ɗaya saduwa dashi ba da izininsa ba, ko da yake har yanzu ba samu ƙwaƙƙwaran bayanai ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Nijar Ta Yanke Wa Ofishin Jakadancin Faransa Ruwa Da Wuta
Laifin aikata luwaɗi dai ya shafi tirsasawa ƙananan yara ko kuma waɗanda ke da wata larura.
Kazalika laifi ne babba auren jinsi wanda ke kai saura yaɗa cuta mai karye garkuwan jiki ta HIV ko kuma wani laifi mai kama da haka.
Ƙasar Uganda dake gabashin nahiyar Afirka dai na daga cikin kasashen duniya dake da tsauraran dokoki kan haramta auren jinsi, inda duk wanda aka cafke da taka wannan doka toh hukuncin kisa ne a kansa.
Kasashen duniya da dama sun soki matakin majalisar dokokin na Uganda inda har ya kai ga bankin duniya ya dakatar da lamuni kudi da yake baiwa ƙasar a farkon watannan.
Wannan ba shine mutum na farko da aka cafke da laifin aikata luwaɗi ba, domin koda a farkon wannan wata ma dai an yi nasarar cika hannu da wasu mutanen.
Rabon da ƙasar Uganda ta aiwatar da hukuncin ƙisa dai tun 2005 to amma ba ta daina aiwatar da hukunci kan aikata manya laifuka ba.