Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, a yayin da yake jawabi ga mahalarta taron Manoman Yobe a dakin taro na Banquet Hall, dake gidan gwamnati A Damaturu, ya jaddada manufar gwamnatinsa na bunkasa harkokin noma da kiwo.
Ya kuma bayyana cewa hakan zai ba da damar samar da ayyukan yi da wani dawwamammen tsari da zai ci gabantar da jihar. Gwamnan ya ce jihohi da dama a kasarnan, da kuma mafi yawan mutanen Yobe suna ayyukan noma a matsayin hanyar samun kudaden shigar su. Inda ya ce; wannan ya nuna cewa harkar noma na daya cikin hanyoyin bunkasa tattalin arziki.