A ranar Laraba ne gwamnatin tarayya ta umurci hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya NCAA da ta sanyawa kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa takunkumin da aka ce sun ki sayar da tikiti a Naira domin kare muradun ‘yan Najeriya. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ne ya sanar da hakan ga manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu Ya Taya Sabuwar Firaministar Burtaniya Murna
Ya ce bayanan sirri sun nuna cewa wasu daga cikin kamfanonin jiragen sun ki amincewa da Naira da kuma domin biyan kudin tikitin su da Dala wanda ya saba wa dokokin kasar nan.
Ya kara da cewa, hukumar ta NCAA an ba ta damar tunkarar duk wani kamfanin jiragen sama da ya karya dokar da gangan.
Ya ci gaba da cewa, wasu daga cikin kamfanonin jiragen sun kuma hana hukumomin shiga gidajen yanar gizon su don yin mu’amala, inda suka zabi fitar da tikiti masu tsada.
Ya yi gargadin cewa duk wani mai keta wannan doka, komai girman matsayin sa, ba zai tsira ba idan an kama shi.
Hadi ya kuma ce, kamfanonin jiragen sama na kasashen waje sun samu sama da dala biliyan 1.1 daga Najeriya a shekarar 2016 lokacin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ware dala miliyan 600 da ta gada daga gwamnatin da ta shude.
Ministan ya kara da cewa sama da dala miliyan 265 ne kuma aka bai wa kamfanonin jiragen sama a bana daga cikin kimanin dala miliyan 484 da aka ware musu.
Sirika ya ja kunnen kamfanonin jiragen sama da su guji yin amfani da kafafen sada zumunta wajen biyan bukatunsu maimakon bin hanyoyin diflomasiyya.
Ya yi watsi da rahoton da ke cewa gwamnati ta kashe sama da Naira biliyan 14.6 na kudadenta kan aikin jirgin Najeriyar duk da cewa tana da hannun jarin kashi biyar kacal a kamfanin.
Ya ce gwamnati ta saki Naira miliyan 651 ne kawai don bayar da shawarwarin kasuwanci da hukumar ta FEC ta amince, amma har yanzu ba ta bayar da na biyu ba saboda har yanzu masu ba da shawara ba su gama aikinsu ba.
Sirika, yayin da yake bayar da karin haske kan kamfanin na Najeriya Air, ya ce gwamnati ta kudiri aniyar kafa kamfanin.
A WANI LABARIN KUMA: Rikicin PSC Da NFP: Mu Za Mu Ci gaba Da Daukar Sabbin Yan sanda—PSC
Hukumar kula da aikin ‘yan sanda ta kudiri aniyar ci gaba da daukar sabbin jami’an ‘yan sanda duk kuwa da matakin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta dauka.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa an samu rashin jituwa tsakanin hukumar ta PSC da hukumar NPF, musamman babban sufeton ‘yan sanda, Usman Baba kan daukar sabbin ‘yan sanda aiki.