Alhaji Ibrahim Salisu, Daraktan hukumar lura da tsaftace ruwa na jihar Kano wato RUWASA a takaice, ya bayyana cewa hukumar ta su za ta samar da tsaftataccen ruwan sha a dukkanin kananan hukumomin da ke jihar. Alhaji Ibrahim Salisu, sabon Daraktan hukumar, ya bayyana hakan ne jim kadan da fara aikinsa a ranar Litinin a Kano. Ya kuma yi alkawarin samun hadin kan dukkanin masu ruwan da tsaki domin ganin an samar da ingantacce kuma tsaftataccen ruwan sha ga al’ummar jihar Kano baki daya. Ya ce; zai yi aiki tukuru wajen cimma haka. Ya kara da cewa; za su samar da burtsatse na zamani ciki har da wanda ke amfani da rana wato Solar da famfuna domin al’umma su samu dama cikin sauki wajen samun ruwa. A karshe ya mika godiyarsa ga Gwamna Dk. Abdullahi Ganduje bisa zabo shi ya bashi wannan mukamin.